Al'umma

Tirƙashi: Ido da harshen gawar wata mata sun bace

An samu tashin hankali a Ogbe-Ani, Ubulu-Uku, a karamar hukumar Aniocha ta Kudu a jihar Delta, sakamakon kin amincewa da wata gawa da aka kawo ba tare da ido, harshe da sauran gabobin jikin ta ba.

Marigayiyar mai suna Misis Comfort Biakpara, wacce ta kai kimanin shekaru 50, an ce mijin nata wanda ya fito daga karamar hukumar Burutu ta jihar ne ya kawo ta gidan danginta dake Ubulu-Uku.

An tattaro cewa an kwantar da marigayiyar a gidan ta a ranar Assabar don dubawa lokacin da aka gano cewa wasu muhimman gabobin sun bace.

Advertisement

Wata majiya mai tushe ta shaida wa wakilin The Punch cewa lamarin ya haifar da fargaba a cikin al’umma, domin matasa da dattawan sun ce gawar ba yar su ba ce.

“Ya yi muni jiya (Asabar). An kawo yar uwar mu ba tare da idanu, harshe da sauran gabobi ba.

“Yayin da suka kwantar da yar uwar mu a kan wani benci a cikin rufaffen wuri kuma yan uwa da sauran mutane za su ganta, abin takaici, mun fara gano cewa an sanya auduga a idon ta.

“Lokacin da muka daga sanar da mutane muka kara bincike, sai muka gano cewa babu idanu kuma a lokacin ne matasa suka tayar da zaune tsaye suka fara bazuwa ko’ina. Wasu sun sami ƙananan raunuka a cikin lamarin.

“’Yan uwan mijin da suka kawo gawar sun gudu ne saboda mun fusata da wannan lamari da ya faru. Daga baya mun gano cewa hatta harshen ta ma an cire shi,” inji majiyar.

Majiyar ta bayyana cewa mijin mamacin ba ya nan.

An tattaro cewa an yi watsi da gawar a rumfar har zuwa karfe 8 na dare inda aka kai ta dakin ajiyar gawa tare da taimakon wasu yan banga a cikin al’umma.

Majiyar ta ce an shirya ‘yan uwa ne domin yin fito-na-fito da mijin wanda abin ya shafa.

Advertisement