Siyasa

Tinubu ya gana da jiga-jigan Sanatocin APC a Majalisar Dattawan Najeriya

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata Ahmed Bola Tinubu yana gana da yan majalisar dattawa na APC.

Tinubu ya isa harabar majalisar ne da misalin karfe 2:26 na rana domin ganawa da yan majalisar a babban zauren majalisar wanda tun farko aka sanar a zauren majalisar a ranar Laraba.

Arewa Times Hausa ta lura cewa Tinubu ya iso da ayarin motoci, zuwan na shi ya zama zagon kasa ga idanun ma’aikata da maziyartan Majalisar a ranar Laraba.

Tinubu dai tsohon Sanata ne kuma galibin Sanatoci a dandalin jam’iyyar APC ne suka halarci taron, ciki har da uwargidan shi, Sanata Oluremi Tinubu wadda ta dade tana jira a dakin taro na 301, wurin taron.

Advertisement