Tinubu Ya Amince Da N70,000 A Matsayin Albashi Mafi Ƙaranci
A ranar Talata ne Shugaba Bola Tinubu ya amince da Naira 70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya.
Tinubu, wanda ya bayar da amincewar a wata ganawa da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin albashi na kasa duk bayan shekaru uku.
Wata sanarwa da mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce: “Shugaba Tinubu ya kuma yi alkawarin samar da hanyoyin da za su taimaka wa kamfanoni masu zaman kansu da kuma kananan hukumomi wajen biyan mafi karancin albashi.
“Shugaba Tinubu ya bayyana wannan matsayar ne a taron da ya yi da shugabannin TUC da NLC ranar Alhamis a Abuja, karo na biyu da bangarorin suka hadu a cikin kwanaki 7.
“Shugabannin kungiyar kwadagon sun yabawa shugaba Tinubu bisa irin wannan hali na uba kamar yadda shugaban kasar ya kuma yi alkawarin yin amfani da karfin ikonsa wajen biyan bukatun kungiyoyin jami’o’in na neman albashin watanni 4 da ba a biya su ba.”
Batun mafi karancin albashin ma’aikata na kasa ya kasance abin cece-kuce tsakanin shugabannin kwadago da gwamnatin tarayya a ‘yan watannin da suka gabata.
Kungiyar kwadagon ta tsunduma yajin aikin ne bayan ta kasa cimma matsaya kan albashin da gwamnatin tarayya ta yi.
Kungiyar kwadago ta nemi a biya ta N494,000 a matsayin albashi karami, amma ta koma N250,000 bayan da gwamnatin tarayya ta yi gaba da baya.
Sai dai gwamnatin tarayya ta dage kan biyan N62,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi kafin amincewar Tinubu na N70,000.