Siyasa

Tikashi Kwankwaso da Peter obi Zasu Hade Kansu Domin Cin Takarar Shugaban Kasa

Tikashi Kwankwaso da Peter obi Zasu Hade Kansu Domin Cin Takarar Shugaban Kasa

Dan takara shugaban Najeriya na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce yana tattaunaa da takwaransa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi domin yiwuwar hada gwiwa a zaben 2023.

Ya bayyana haka ne a tattaunaarsa da BBC Hausa.

A cewarsa “gaskiya muna magana da shi Peter Obi, ko kuma ma in ce kwamiti yana aiki domin ya duba dukkan abin da ya kamata (kan hada gwiwa da shi), kuma abokai da ‘yan uwa suna zuwa suna yi mana magana kan batun.”

Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya ce hada gwiwarsu tana da muhimmanci musamman ganin cewa jam’iyyun APC da PDP ba su tsayar da dan takarar mataimakin shugaban kasa daga yankin kabilar Igbo ba.

gadai Bidiyon tattauna war tasu akasa ⬇️

Back to top button