Siyasa

Taron Ƙasa: APC za ta fara sayar da fom a 14 ga watan Fabrairu

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta fara siyar da fom ga masu neman shugabancin kasa a babban taron kasa mai zuwa daga ranar 14 ga watan Fabrairu.

Za’a gudanar da babban taron jam’iyyar APC na kasa a ranar 26 ga Fabrairu.

Sakataren jam’iyyar APC na kasa mai rikon kwarya da tsare-tsare na musamman John Akpanudoedehe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Advertisement

Ya kuma bayyana jadawalin ayyukan taron.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Jam’iyyar APC CECPC a taronta na yau da kullum karo na 19 a ranar Laraba, 19 ga watan Junairu, 2022, a sakatariyar jam’iyyar ta kasa ta yi nazari tare da zartar da jaddawalin ayyukan da za a gudanar a ranar 26 ga Fabrairu, babban taron jam’iyyar APC na kasa.

“Karbar rahoton wucin gadi na kwamitin sulhu na kasa zai gudana ne a ranar 31 ga Janairu, 2022.

“Bincike da amincewa da Rahoton Majalisun Jihohi – Fabrairu 2, 2022.

Kaddamar da Shugabannin Jaha – Fabrairu 03, 2022.

“Sayar da fom ga duk masu neman mukaman kasa a Sakatariyar APC ta kasa – 14 ga Fabrairu, 2022.

“Bayar da cikakkun fom da takaddun rakiyar a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a ranar 19 ga Fabrairu, 2022 ko kafin nan.

“Buga ƙananan kwamitoci – Fabrairu 19, 2022.

“Ana duba duk masu son tsayawa takarar ofisoshi na kasa – 20 ga Fabrairu – 22 ga Fabrairu.

Neman Ƙorafe-ƙorafe don saurare da warware korafe-korafe da suka taso daga aikin tantancewar – Fabrairu 23, 2022.

“Kaddamar da dukkan wakilai na doka da zaɓaɓɓun wakilai zuwa Babban Taron Kasa – Fabrairu 24 zuwa 25 ga Fabrairu, 2022.

“Taron kasa don zabar jami’an kwamitin zartarwa na kasa – Fabrairu 26, 2022.

Advertisement