Tarihi

Tarihin Sheikh Muhammad Hamidullah

Daga Shafin Isma’il Ibrahim El-kanawy

”Sheikh Muhammad Hamidullah, Al-Haidar shine shehun malamin da yaki amsar kyautar gimamawa da lambar yabo na Sarki Faisal na Saudiyya a shekarar 1994, yana mai cewa:

“Ni ban rubuta abin da na rubuta ba face sai saboda Allah, ku bar ni kada ku lalata min aiki na”.

Wannan bawan Allah dubban mutane ne suka musulunta a hannunsa a kasar Faransa da kewayenta, a shekaru hamsin da yayi a cikinta.

Yana jin harsuna 22, yare na karshe da ya koya shine yaren “Thai” na kasar Thailand, a lokacin yana da shekaru 84 a duniya.

An bayyana cewa bai taba yin aure ba a rayuwarsa, ilimi kawai ya aura da kuma kiran mutane zuwa ga addinin Allah, sai Allah ya yiwa auren albarka; saboda ya haifi litattafai sama da 450 da ya rubuta da yaruka daban daban, ya kuma tarjama litattafai da makaloli sama da 937 suma daga harsuna daban daban.

Da kansa yake yiwa kansa bukatu, kamar wanke kayan sawa da kwanukan cin abinci da sauransu, baya yarda wani yayi masa daga dalibansa; duk kuwa da irin ilimi da daukakar da Allah ya bashi a wannan yankin.

A lokacin da ya samu kyauta da lambar yabo mafi kololuwa ta Pakistan, daga hannun tsohon prime minister marigayi Muhammad Dhiya’ul haqq, akan irin gudunmowa da ya bayar ta bangarori da dama musamman bangaren addini da tarihi, kai tsaye ya bayar da kyautar kudaden da ya samu ta hanyar lambar yabon ga wata makarantar koyar da ilimin addinin Musulunci a Islamabad, wanda a lokacin kudin sun kai kimanin Rupee miliyan daya, a lokacin ne ya fadi wata magana mai bank`aye wacce tarihi ya taskace ta, inda yake cewa:

“Da ace na karbi wannan kyautar a wannan duniyar mai karewa, toh da bansan me zan samu na lada kuma a wancan gidan na lahira ba wanda yake matabbaci”.

Sheikh Muhammad Hamidullah Al-haidar Abady Al-hindy. Ya rasu a shekara ta 2002, yana mai shekaru 94 a duniya.

Advertisement