Al'umma

Tarihin Dahiru Mangal: Daga Direban Motar Dakon Kaya Zuwa Hamshaƙin Mai Kuɗi

Kasuwanci mai nasara ba haka kawai yake faruwa ba. Yawancin lokaci yana ɗaukar ra’ayin kasuwanci na dabaru da ɗan kasuwa mai wayo ya aiwatar da su don wanzuwar hakan. Musamman ga wani yanayi irin na Najeriya da a kullum kasuwanci ke fuskantar kalubalen da ke barazana ga hada hada.

Daya daga cikin hazikan ’yan kasuwa daga Arewacin Najeriya shi ne Dahiru Mangal, wanda a baya aka karrama shi da lambar yabo ta kwamandan kasuwanci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar domin bunkasar harkokin kasuwanci a Najeriya.

An haife shi a ranar 3 ga Agusta, 1957, ga iyalan Alhaji Barau Mangal da ke Jihar Katsina, Mangal ya halarci makarantar firamare ta Gafai, ya kammala a nan a shekarar 1971. Ya ci gaba da samun digiri na uku a makarantar koyar da larabci ta Kastina. Ya kammala karatunsa a shekarar 1976.

Mangal ya kasance yana da burin zama dan kasuwa mai nasara, don haka ya himmatu wajen harkar sufuri. Ya fara a matsayin direban babbar mota, daga nan ya sayo motocinsa ya yi haya. A cikin ’yan shekaru, Mangal ya sami damar kafa kansa a matsayin babban hamshakin dan kasuwa, inda ya shiga kasuwanci da dama a sassa daban-daban na Nijeriya.

A yau, harkokin kasuwancin Mangal sun katsa hanyoyin sufuri, gine-gine, da man fetur da iskar gas. A shekarar 2006, ya kafa kamfanin Max Air (wanda aka fi sani da Mangal Airlines), babban kamfanin jirgin saman Najeriya da ke gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida da na shiyya da kuma na kasa da kasa tare da hadin gwiwar wani kamfani na kasar Sin, Mangal Industries Limited na gina kamfanin siminti miliyan 3 a kowace shekara a Jihar Kogi.

Aikin wanda aka shirya kammala shi a shekarar 2024 an kashe jimillar dala miliyan $600. Wannan shi ne abin da ya ce game da aikin.