Tsaro

Takardun Koke: An bukaci Biden da ya rufe gidan yarin soja na Guantanamo

Hoto: Tutar Amurka a cikin zagayen Guantanamo

Fiye da mutane 30,000 ne suka rattaba hannu kan wata takardar koke da ke neman shugaban Amurka Joe Biden da ya rufe sansanin na Guantanamo Bay da aka kafa a shekarar 2002 lokacin gwamnatin tsohon shugaba George W. Bush.

Advertisement

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amurka ce ta fara gabatar da koken, mai kiran Guantanamo a matsayin “lalacewar hakkin dan Adam”.

“Shekaru 20, gidan yarin sojojin Amurka da ke Guantanamo Bay ya zama tabo ga kasarmu. A yau, maza musulmi 39 suna ci gaba da tsare har abada a can, kan kudin falaki dala miliyan 540 a duk shekara,” in ji ta.

Advertisement

Gidan yarin, wanda ke cikin sansanin sojin ruwa na Guantanamo Bay na Amurka da ke kudu maso gabar tekun Cuba, an kafa shi ne bayan harin da aka kai wa Amurka a ranar 11 ga watan Satumba. An yi amfani da shi wajen tsare wadanda ake zargi da ta’addanci har abada, wadanda wasunsu ke jiran shari’a. Gwamnatin Cuba ta ce sansanin ya sabawa doka.

Tun daga watan Janairun 2002, kusan mutane 779 maza da yara maza musulmi ne ake tsare da su a Guantanamo. An tsare akasarinsu ba tare da tuhuma ko kuma gurfanar da su a gaban kotu ba, kuma an azabtar da da yawa kamar yadda kafafen yada labarai da wani jigo a gwamnatin Bush suka bayyana.

Kimanin mutane 540 ne aka saki a lokacin gwamnatin Bush, wasu 200 ko fiye kuma an sake su a lokacin gwamnatin Obama, daya kuma a lokacin gwamnatin Trump. Mutane tara sun mutu a sansanin, in ji ACLU.

Daga cikin mutane 39 da ake tsare da su, 12 ana tuhumar su da laifukan yaki. Daga cikin wadanda aka yankewa hukunci biyun kuma 10 na jiran a gurfanar da su gaban kuliya. An tsare fursunonin takwas a gidan yari na yaki, yayin da wasu 19 kuma ake tsare da su a gidan yari, amma an ba da shawarar a kai su wata kasa idan an cika sharuddan tsaro, a cewar kundin Guantanamo, in ji jaridar New York Times. .

Advertisement