Al'umma

Taimakon jinƙai na farko ga Ukraine ya isa Poland Alhamis – WHO

A ranar alhamis ne jigilar kayan agaji na farko ga Ukraine zai isa kasar Poland, inji Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Za’a kai ton shida na kula da raunuka da kuma kayyakin tiyata na gaggawa don biyan bukatun majinyata 1,000, da sauran kayayyakin kiwon lafiya don biyan bukatun mutane 150,000, in ji Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a wani taron manema labarai a Geneva.

Ya kuma jaddada bukatar samar da hanyar jin kai don tabbatar da cewa kayayyakin sun isa ga mutanen da suka fi bukata.

Advertisement
Advertisement