Taɓawa Da Kallon Nonon Mata Akai-Akai Yana Ƙara Tsawon Rayuwar Maza – Dr. Karen

Wani masanin kimiya dan kasar Jamus, Dr Karen Weatherby ya yi gwaje-gwajensa da bincikensa cewa tabawa da kallon nonon mata yana kara tsawon rayuwar maza.

Binciken wanda aka shafe tsawon shekaru biyar ana gudanar da shi, ya kunshi maza 500, inda aka umurci rabinsu da su rika kallon nonon mata ta hanyar sha’awa na tsawon mintuna 10 a kowace rana yayin da sauran rabin kuma aka umurce su da su kaurace wa yin hakan.

Binciken ya nuna cewa mazan da suke kallo ko taba nono na mata sun nuna raguwar matsalolin zuciya, rage yawan bugun zuciya da rage hawan jini yayin da yake kara tsawon rayuwar namiji da kuma baiwa namiji damar yin rayuwa mai kyau.

“Mun yi imanin cewa ta yin hakan akai-akai, matsakaicin mutum zai iya tsawaita rayuwarsa na tsawon shekaru hudu zuwa biyar,” in ji masanin kimiyyar Jamus.

Ya buga a New England Journal of Medicine, ya bayyana cewa kallon nonon mata yana da lafiya kuma yana kara tsawon rayuwar maza.