Al'umma

Sokoto: Wani Kansila ya rabawa mutanen mazabar shi tabarmi biyu da Ƙwallo ɗaya

Wani Kansila karkashin gwamnatin Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya raba tabarmi biyu da kwallo ɗaya ga al’ummar mazabar shi.

Kansilan Kebbe ta gabas Honourable Aliyu Garba ya raba tabarmin biyu ne ga al’ummar mazabar shi a garin Sadada a kokarin sa na kyautatawa al’ummar yankin vda su ka zabe shi a matsayin Kansila lokacin zabukan kananan hukumomin da ya gabata a jihar.

A ya yin bikin karbar yabarmin, al’ummar yankin na Sadada sun nuna farin cikin su da samun wannan kyauta daga Kansilan.

Advertisement

Daga: Mustapha Ahmad Dukura.

Advertisement