Tsaro

Sokoto Ta Zama Mafakar Ƴan Bindiga, Yayin Da Ƴan Bindigar suka Kashe Ƴan Sanda 3 Da Sauran Su – Ibrahim

A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki kasuwar mako-mako ta ‘Yar Bulutu da ke karamar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane shida ciki har da ‘yan sanda uku.

Harin dai ya zo ne a ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je jihar domin kaddamar da taron shugaban hafsan sojin kasa na 2022.

An ce ‘yan bindigar sun kai hari kasuwar ne da misalin karfe 12:30 na rana.

Advertisement

Dan majalisar mai wakiltar Sabon Birni ta Kudu a majalisar dokokin jihar, Sa’idu Ibrahim, ya shaida wa yan jarida cewa ‘yan bindigar sun zo ne a kan babura kusan 20 tare da kowane babur dauke da mutum uku.

“Da farko sun je inda ’yan sandan tafi da gidan ka (MOPOL) da ke jagorantar kasuwar suke a tsaye. Sun kashe biyu daga cikin su tare da kona motocin su daya.

“Daga baya sun kashe wani dan sandan da ya ruga cikin daji, suka zaro gawar shi daga daji suka jefa a cikin motar da ke konewa. Sun kuma kashe wasu mutane uku a kasuwar tare da jikkata wasu da dama.

“A yanzu haka ina tare da daya daga cikin ‘yan uwana a asibitin Orthopedic dake Wamakko saboda maharan sun harbe shi a kafar shi,” in ji shi.

Ibrahim ya kara da cewa ‘yan bindiga ne suka kai harin da suka tsere sakamakon hare-haren da sojoji suka kai a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna.

“Ya kamata a gudanar da aikin a duk jihohin da ake fama da ‘yan fashi a yankin Arewa maso Yamma a lokaci daya amma saboda ba a Sokoto ake yi ba, yanzu jihar ta zama mafakar ‘yan bindigar da aka tarwatsa a jihohin,” in ji shi.

Mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Idris Danchadi, wanda ya fito daga yankin yace har yanzu wasu wurare a Sabon Birni na hannun ‘yan fashi.

Advertisement