Siyasa

Sokoto: Kotu ta ɗage zaman sauraron ƙara akan rikicin shugabancin APC

Kamar yanda Sakkwatawa suka sani cewar, a yauma za’ayi zama a Kotu kan shari’ar jam’iyar APC ta jihar Sokoto kuma tabbas yanzu haka anan Abuja an kammala sauraren bayanai da zaman kotu na yau a shari’ar ta jam’iyar APC ta Sokoto a kotun Appeal Court dake Abuja.

Amma a zance na gaskiya ba’a yanke kowane hukunci ba ayau kamar yanda wasu ke cigaba da yayatawa cewar anyi hukunchi a shari’ar jam’iyar APC ta jihar Sokoto.

Haka zalika, Alkalin kotun ya bayyana cewar gobe Talata za’a cigaba da gudanar da wannan shari’a kamar yanda kotu ta bayyana ayau.

Advertisement
Advertisement