Tsaro

Sojojin Yukren sun yi galaba a kan sojojin Rasha

Sojojin Ukraine sun yi ikirarin cewa sun yi nasarar fatattakar wani rukunin sojojin Rasha tare da kashe kwamandan su, Col. A. Zakharov.

An ce sun samu nasarar ne a garin Brovary dake arewa maso gabashin Kyiv.

Ma’aikatar tsaron Ukraine ta fada a ranar Alhamis cewa “An kori kwamandan rundunar ‘yan mamaya, Kanar Zakharov.

“A yayin yakin da aka yi a gundumar Brovary na yankin Kyiv, kungiyar bataliya ta (BTGr) na runduna ta 6 (Chebarkul) na runduna ta 90 na rundunar ta tsakiya ta yi asarar ma’aikata da kayan aiki,” ma’aikatar ta bayyana a shafinta na Twitter.

Back to top button