Tsaro

Sojojin Ukraine sun harbo jiragen yakin ƙasar Rasha

Sojojin Ukraine sun fada a ranar Talata cewa sun harbo jiragen yakin Rasha da dama yayin da Rasha ta mamaye makwabciyarta ta ya shiga kwana na shida.

An harbo jiragen yakin Rasha 5 da wani jirgin sama mai saukar ungulu yayin harin ta sama a ranar litinin, kamar yadda jaridar Ukrayinska Pravda da rundunar sojin sama ta Ukraine suka ruwaito.

An ce an harbo jiragen ne a lokacin da aka kai hare-hare ta sama a garuruwan Vasylkiv da Brovary da ke yankin Kiev, kuma an harbo wani makami mai linzami da wani jirgin sama mai saukar ungulu a kusa da Kiev.

Advertisement

An bayar da rahoton cewa jiragen yakin Ukraine sun harba makamai masu linzami da bama-bamai kan tankokin yaki da sojojin Rasha a kusa da Kiev da kuma kusa da birnin Zhytomyr.

Rahotanni sun ce an jefa bama-bamai a yankin Chernihiv da ke arewacin kasar da kuma birnin Berdyansk na kudancin Ukraine, wanda a halin yanzu ke karkashin ikon Rasha.

A halin da ake ciki, Hotunan tauraron dan adam sun nuna jerin gwanon motocin sojojin Rasha da aka kiyasta tsawon kilomita 64 sun nufi Kiev babban birnin kasar Ukraine, a cewar kamfanin dillancin labaran Ukraine UNIAN.

Advertisement