Siyasa

Sojojin Uganda sun musanta murabus din ɗan shugaban ƙasa daga aikin Soja

Manjo Janar Muhoozi Kainerugaba, hagu, da matarsa Charlotte Kutesa Kainerugaba, dama

Rundunar sojan Uganda tace dan shugaban kasar Yoweri Museveni, Laftanar-Janar, wanda ake kyautata zaton zai maye gurbin mahaifin shi da ya dade yana mulki, bai yi murabus ba.

Advertisement

Muhoozi Kainerugaba ya sanar a shafin shi na Twitter a ranar 8 ga watan Maris cewa yayi ritaya daga aikin soja bayan kusan shekaru talatin yana aiki. Mahaifin shi ya kasance shugaban kasar da ke gabashin Afirka tun shekara ta 1986.

An fassara sakon ta twitter a matsayin wata alama da ke nuna cewa Kainerugaba, kwamandan sojojin kasa na kasa, na shirin shiga harkokin siyasa a kan hanyar da za ta iya tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa a 2026.

Advertisement

Advertisement