Tsaro

Sojojin Mali 27 sun mutu a wani hari da ƴan tawaye suka kai a barikin sojoji

Wani harin da yan tawaye suka kai kan wani sansanin soji da ke tsakiyar kasar Mali a ranar Juma’a, yayi sanadin mutuwar sojoji akalla 27 tare da raunata wasu 33, gwamnatin kasar ta kuma kara da cewa akalla sojoji bakwai ne har yanzu ba a gansu ba bayan wani hadadden harin da aka kai a kauyen Mondoro, wanda ya hada da mota da bama-bamai.

Advertisement

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce an kashe “’yan ta’adda saba’in” a cikin martanin da sojojin suka mayar a ranar Juma’a, ba tare da bayyana ko wace kungiya ce ke da alhakin kai harin ba.

Ƙungiyoyin al-Qaeda da na ISIL (ISIS) suna aiki a tsakiyar Mali.

Advertisement

Sansanin Mondoro yana kusa da kan iyakar Mali da Burkina Faso kuma a baya ‘yan tawayen da ke yaki da gwamnatin Mali da dakarun kasashen waje sun kai hari.

Kimanin sojoji 50 ne suka mutu bayan wani hari da aka kai Mondoro da kuma sansanin Boulkessi da ke kusa a watan Satumbar 2019.

Advertisement