Tsaro

Sojojin Aljeriya sun kashe yan ta’adda 7 a wani samame da suke cigaba da yi

Dakarun sojojin kasar Aljeriya sun kashe wasu mutane 7 da ake zargin yan bindiga ne a ranar Asabar a wani samame da suke cigaba da yi a lardin Skikda dake Arewa Maso Gabashin kasar, inji ma’aikatar tsaron Algeriya.

Ma’aikatar tsaron kasar ta kara da cewa, an harbe yan ta’addan 7 ne a yayin wani samame da aka gudanar a cikin dazuzzukan gundumar Collo ranar assabar.

Sojojin na kasar Aljeriya akai-akai suna bayar da rahoton manyan hare-hare suke aiwatarwa kan mayakan masu tsatsauran ra’ayi, shekaru 20 bayan kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru 10 ana gwabzawa tsakanin gwamnatin kasar da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane dubu 200,000.

Advertisement

Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da sulhu da aka rattabawa hannu a shekara ta 2005 don kawo karshen tashe tashen hankula, har yanzu kungiyoyi masu dauke da makamai suna kai hare-hare na lokaci-lokaci kan jami’an tsaro a kasar.

Advertisement