Al'umma

Sojan Sama a kotu bisa laifin kashe miliyan ₦20 da aka tura asusun shi bisa kuskure

A ranar Talata ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta shiyyar Kaduna ta gurfanar da wani sojan sama mai suna Lance Kofur Haruna Samuel na rundunar sojojin saman Nijeriya dake Kaduna a gaban Mai shari’a Darius Khobo na babbar kotun jihar Kaduna dake zamanta a Kaduna a kan tuhume-tuhumen da ya shafi sata da almundahana.

A ranar 3 ga watan Disamba, 2020 wanda ake tuhuma ya karbi alat shaidar kiredit na kudi ₦20,014,300 da aka biya a asusun ajiyar sa na banki. An ce an aika da kudin ne bisa kuskure daga asusun wadanda suka dauke shi aiki.

An bayar da rahoton cewa wanda ake tuhuma ya cigaba da cire wani bangare na kudin don amfanin kansa, gami da daidaita basussuka.

Advertisement

An kuma zargi wanda ake tuhuma da gudu daga bakin aikinsa zuwa jihar Filato inda daga karshe jami’an Hukumar suka kama shi.

Tuhuma daya daga cikin tuhume-tuhumen da ake yi kan wanda ake tuhuma ta bayyana kamar haka: “Kai Haruna Samuel wani lokaci a cikin watan Disamba 2020 a Kaduna dake karkashin ikon wannan Kotu ka karkatar da kudi ₦20, 014,300.00 (Miliyan Ashirin da Dubu Sha Hudu, Naira Dari Uku). Mallakar NAF Ground Training Centre da aka aika da kuskure zuwa asusunka na Zenith Bank mai lamba 2189705893.

Ka aikata laifin da ya saba wa sashe na 293 na dokar hukunta manyan laifuka ta jihar Kaduna, 2017, 2017 kuma hukuncin da za a yanke masa. Sashe na 294 na wannan doka”.

Wanda ake tuhumar ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa da shi lokacin da aka karanta masa.

Dangane da rokonsa, lauyan masu shigar da kara, Precious C. Onyeneho, ya roki kotun da ta sanya ranar da za a fara shari’ar. Sai dai lauyan dake kare wanda ake zargin, S.A Yahaya ya bukaci kotu ta bayar da belin wanda yake karewa.

Mai shari’a Khobo ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi ₦5, 000,000.00 (Naira Miliyan Biyar) da kuma wani amintaccen wanda zai tsaya masa.

Advertisement