Al'umma

Soja ya lakada wa wani tsoho duka har ya mutu akan kuɗin gyaran Rediyo

Hoto: Domin misali

A wani labarin da jaridar Punch ta wallafa a safiyar yau, an ruwaito cewa wani soja da ba’a tantance ba ya kashe wani tsoho mai shekaru 69, wanda aka bayyana sunan shi da Mista Philip Ajayi, AKA ‘Odua’. biyo bayan rashin fahimtar da ya faru a tsakanin su a Akure, jihar Ondo.

Bayanin da Punch ta samu ya nuna cewa wanda ake zargin kwanaki biyu da suka gabata ya baiwa marigayin rediyon shi ya gyara kuma a ranar da sojan ya dawo karban rediyon, Odua ya shaida masa cewa an riga an kammala kashi 80 cikin 100 don haka ya kamata a yi hakuri amma sojan ya bukaci a mayar masa da kudin shi ₦7,000, kuɗin da marigayin ya kasa ba shi, a dalilin haka sai ya farmai.

An bayyana cewa sojan ya fara dukan dattijon mai shekaru 69 da haihuwa har sai da ya kasa motsi, kafin daga bisani ya mutu yayin da wanda ake zargin ya gudu.

Lokacin da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Ondo ke mayar da martani kan wannan mummunan lamari, Misis Fumilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce, har yanzu jami’an yan sanda ba su samu cikakken bayani kan wanda ake zargin ba, domin tabbatar da ko na gaske ne ko sojan karya.

Advertisement