Siyasa

Shugabancin APC: Ba zan janye wa ɗan takarar Buhari ba – Al-Makura

Biyo bayan zargin amincewa takarar Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, a matsayin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari yayi, Sanata Tanko Al-Makura, wanda kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa ne, ya sha alwashin ba zai janye daga takarar shugabancin jam’iyyar ta All Progressives Congress (APC).

Ko da yake an ce wasu masu neman kujerar sun janye don ganin sun goyi bayan da dan takarar da shugaban kasa ke mara wa baya, yayin Al-Makura yaci gaba da zafafa yakin neman zaben shi a matsayin shugaban jam’iyar APC na kasa.

Al-Makura, yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, yace rahoton cewa Buhari ya amince da wani dan takara, hasashe ne kawai.

Advertisement

“Madogarar bayanan ba sahihai ba ne. Ba na gaske ba ne. Kuma na san abin da Shugaban kasa yake nufi, a koyaushe yana tsayawa kan abin da ya dace da kuma tsarin da ya dace. Kuma sai dai idan ina da madaidaicin tushen bayanin da ke bayyane. Har yanzu ina da shakka. Ina da hanyoyi da yawa da zan iya kaiwa ga shugaban kasa da mutanen da ke kusa da shi.

“Kuma tun da waɗannan hasashe ba su zo ta waɗannan hanyoyin ba, ina ɗaukar su a matsayin hasashe. Shi yasa a lokacin da nake magana da ku yakin neman zabe na yana tafiya ne da wani lokaci daban, domin ganin yakin neman zabe na yayi nisa domin jiran mataki na gaba kamar yadda shugabannin jam’iyyar suka umarta,” inji shi.

Advertisement