Tsaro

Shugaban Ukraine ya bukaci ƴan kasar da su ɗauki makami a yakin da suke da Rasha

Bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar shi, shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ayyana dokar ta-baci a duk fadin kasar, yana mai dagewa cewa Ukraine za ta yi “yaki da fatattakar kowa”.

Advertisement

Da yake jawabi ga yan kasar Ukraine jim kadan bayan Rasha ta harba makamai masu linzami a manyan biranen kasar, Volodymyr ya bukaci al’ummarsa da su kwantar da hankula, yana mai ba da tabbacin kasar za ta fito cikin nasara.

A cewar shi, “An ji karar fashewar abubuwa a garuruwan Ukraine da dama. Muna gabatar da dokokin yaƙi a duk faɗin jihar. Muna aiki. Sojojin suna aiki. Muna da ƙarfi. Mun shirya don komai. Za mu kayar da kowa.”

Advertisement

A wani jawabi da aka yi ta gidan talabijin, Volodymyr ya yi ishara da ayyukan sojojin Ukraine da bangaren tsaro na yin tir da harin da sojojin Rasha ke kaiwa, inda ya bukaci goyon bayan jama’a, gami da dalibai.

“Makasan tsaronmu suna ganin fada da karfi don dakile hare-haren Rasha. Sojojinmu sun ƙunshi mutane masu ƙarfi kuma jama’armu ma mutane ne masu ƙarfi.

Advertisement