Siyasa

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Bwacha ya fice daga PDP

Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Emmanuel Bwacha ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a Najeriya.

Advertisement

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarbi dan majalisar da ke wakiltar mazabar Taraba ta Kudu a zauren majalisar a hukumance a Abuja.

Mai taimaka wa shugaba Buhari kan harkokin sadarwa na zamani da sabbin kafafen yada labarai ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Advertisement

Advertisement