Taskar LabaraiTsaro

Shugaban Marasa Rinjaye A Majalisa Ya Bukaci Buhari Ya Saki Zakzaky Yanzu

Shugaban marasa rinjaye a majalisar tarayya dake Abuja, Mr. Ndudi Elumelu yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya hanzarta sakin malam Ibraheem El-Zakzaky wanda ake tsare da shi sama da shekaru shidda.

Mabiya Zakzaky sun sha yin zanga-zanga daban daban domin ganin an sake malamin, zanga-zangar wani lokacin kan rikide zuwa tashin hankali da yake kaiwa ga hasarar rayuka.

Dan majalisar yayi wannan kiran ne a yau Talata bayan masu zanga-zangar a saki Zakzaky suka datse hanyar shiga majalisa, inda har aka habarto cewa sun harbi wani jami’in tsaron dake gadin hanyar shiga harabar majalisar.

Haka zalika an ruwaito cewa masu zanga-zangar sun farfasa gilasan motoci a majalisar.

Wasu yan majalisar da suka goyawa Mr. Elumelu baya sun bayyana cewa irin yanayin rikicin Zakzaky da sojoji shine ya haddasa Boko Haram a Najeriya.

Idan har kotu ta bada umarnin a saki mutum, ya kamata mu yi kira ga gwamnati da ta sake shi.

Wani dan majalisa daga Jahar Osun, Mr Bamidele Salam yace “cigaba da tsare Zakzaky rashin adalci ne, sannan rashin adalci ga mutum daya rashin adalci ne ga kowa”.

“Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta dubi lamarin Zakzaky domin a tabbatar da bin doka da oda”. Inji Salam.

Back to top button