Siyasa

Shugaban Majalisar Dattawa, Lawan, ya roki gwamnan A’Ibom Udom, da ya koma APC

Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, ya roki gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, da ya duba yiwuwar sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Lawan, wanda yayi wannan roko a Uyo, babban birnin jihar a ranar Asabar, a yayin kaddamar da wata cibiyar shakatawa da Sanata Bassey Akpan ya gina, yace cigaban da Udom ya samu a jihar zai fi dacewa da jam’iyyar a cibiyar.

“Duk da cewa ba a tsarin siyasa daya muke ba, muna jiran ku ku zo ku yi aiki da mu. Muna son zakara kamar ku; babu kunya a tambaya,” inji Lawan.

Advertisement

“Idan ka ga wani abu mai kyau, sai ka ce yana da kyau. Mun ga wani abu mai kyau; don haka m.

“Zan sake zuwa nan saboda akwai abubuwa masu kyau da yawa da za su faru wadanda za su bukaci kasancewar mu ma,” in ji shi

Da yake mayar da martani kan wannan roko, Gwamna Emmanuel ya ce duk da ya yaba da kiran da shugaban majalisar dattawan ya yi masa, bai ga dalilin da zai sa ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC ba domin hakan babban cin amana ne ga al’ummarsa da jam’iyyarsa. wadanda suka yi imani da shi.

Advertisement