Siyasa

Shugaban ƙasar Rasha ya shaidawa Xi, Rasha na son yin shawarwari da Ukraine

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya shaidawa takwaran shi na kasar China Xi Jinping a wani kiran waya da yayi yau Juma’a cewa, Rasha na son yin shawarwari da Ukraine sosai, inji ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin.

Advertisement

China ta ki kiran matakin da Rasha ta dauka a Ukraine “mamaye” ko sukar Rasha duk da tsananta hare-hare da sojojin Rasha ke yi.

Putin ya shaidawa Xi cewa, Amurka da kungiyar tsaro ta NATO sun dade suna yin watsi da halastacciyar matsalar tsaron kasar Rasha, tare da yin watsi da alkawuransu akai-akai, tare da ci gaba da fadada aikin soja zuwa gabas, tare da kalubalantar matakin da Rasha ta dauka bisa manyan tsare-tsare, a cewar wata sanarwa a shafin yanar gizon ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin.

Advertisement

Rasha na son gudanar da shawarwari mai zurfi da Ukraine, in ji Putin.

Advertisement