Siyasa

Shugaban ƙasar Guinea-Bissau, Embalo ya zargi manyan masu hada-hadar miyagun kwayoyi da kitsa juyin mulki

Shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya zargi tsohon hafsan sojin ruwa dake da alaka da safarar miyagun kwayoyi da wasu mutane biyu da ke da hannu a juyin mulkin da bai yi nasara ba a farkon wannan Fabererun nan.

Wasu mutane dauke da muggan makamai sun kai hari kan gine-ginen gwamnati a Bissau babban birnin kasar a ranar 1 ga watan Fabrairu yayin da Embalo ke jagorantar taron majalisar ministoci. Daga baya shugaban ya shaida wa manema labarai cewa ya tsallake rijiya da baya a wani harin bindiga da aka dauki tsawon sa’o’i 5 ana yi ba tare da an samu rauni ba, kuma an kashe mutane 11 akasari daga cikin tawagar jami’an tsaron gwamnati a fadan.

Embalo, wanda ya kaddamar da bincike a kan abin da ya bayyana a matsayin wani shiri mai cike da kudade da kuma yunkurin kisan gilla, ya ce a ranar Alhamis tsohon hafsan sojin ruwa Admiral Jose Americo Bubo Na Tchuto da mukarrabansa Tchamy Yala da Papis Djeme ne suka yi yunkurin juyin mulkin kuma suna daga cikin wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin da aka kama.

Advertisement

Wasu mutane uku da shugaban ya bayyana sunayensu, an kama su ne a watan Afrilun shekarar 2013 a cikin wani jirgin ruwa a gabar tekun yammacin Afirka da wasu jami’an leken asiri na hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar Amurka (DEA) suka yi, bisa zarginsu da hannu cikin wata babbar badakalar safarar miyagun kwayoyi da kuma hada baki a Amurka. tura hodar iblis zuwa Amurka.

Advertisement