Siyasa

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Ramaphosa ya naɗa sabon alkalin alkalai

Cyril Ramaphosa

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya nada kwararre kan harkokin shari’a Raymond Zondo a matsayin sabon alkalin alkalan kasar daga ranar 1 ga Afrilu, 2022.

Naɗin ya fito ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, bayan kammala zaben jama’a.

Zondo, wanda ya rike mukamin mataimakin alkalin alkalai a kotun tsarin mulkin kasar tun shekarar 2017, ya zama fuskar jama’a a yunkurin Ramaphosa na yaki da cin hanci da rashawa a yayin da yake jagorantar wani bincike na baya-bayan nan na kasa kan zargin cin hanci da rashawa a karkashin shugabancin Jacob Zuma, tsohon shugaban kasar.

Advertisement
Advertisement