Labarai

Shugaban Ƙasa Ne Kaɗai Zai Iya Buɗe Iyakoki – Shugaban Kwastam

Kwanturolan hukumar kwastam na Najeriya, Mista Adewale Adeniyi, a ranar Asabar, ya ce shugaba Bola Tinubu ne kadai ke da hurumin sake bude iyakokin kasar.

Ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da makwabta na kan iyaka da Kongolam a karamar hukumar Mai’adua ta jihar Katsina.

Adeniyi, wanda ke mayar da martani game da hargitsin sake bude iyakokin, ya bada tabbacin cewa ana tattaunawa da tuntubar juna dangane da lamarin.

“Da zarar an kammala shawarwari, za a yanke shawara kan lamarin,” in ji shi.

A cewar Adeniyi, Ma’aikatar za ta mayar da hankali ne wajen kawar da cikas da ke yakar kasuwanci cikin ‘yanci daidai da ajandar gwamnatin yanzu na bunkasa tattalin arziki.

Ya ce an yi amfani da matakan da suka dace don rage yawan shingayen binciken kan iyakokin, da inganta hadin gwiwa tsakanin ma’aikatan da ‘yan kasuwa.

“Muna sane da damuwar al’ummomin kan iyaka, musamman dangane da yawan wuraren bincike da kuma rufe iyakokin kasa.

“Ina tabbatar muku da cewa a koda yaushe ayyukan mu suna bin doka ne kawai kuma muna aiki ne da ikon da aka ba su.

“Mun mika damuwa da korafe-korafen mazauna yankunan kan iyaka ga shugaban kasa.

“Saboda yana da kunnuwa, kuma ya ba da umarnin cewa mu saki kayan abinci da aka kwace, da sharadin cewa a kasuwannin Najeriya kawai ake sayar da su,” in ji shi.

Adeniyi ya ce hukumar ta na hada kai da ‘yan sanda da sauran hukumomin makwabta domin magance matsalolin da ke hana fataucin ‘yanci a yankunan kan iyaka.

“Mun san cewa akwai kasuwanni a kusa da iyakokin mu, kuma mun san cewa ba dukkanin su ake nufi da daukar kaya a kan iyakokin kasar ba.

“Za mu ci gaba da sa ido tare da tabbatar da cewa abincin da ake nomawa a Najeriya ya wanzu kuma ana ci a Najeriya. Hakan ya faru ne saboda muna cikin wani yanayi na gaggawa na kasa wanda ke da alaka da karancin abinci.

“Don haka ne ma ya zama dole mu hada kai don taimakawa gwamnati wajen aiwatar da dokoki daban-daban da suka hana fitar da kayan abinci a wannan lokaci,” in ji shi.