Siyasa

Shirye-shiryen Buhari na tallafawa talakawa bututu ne na satar kudi – Gwamna Mohammed

Gwamnan jihar Bauchi, Senator Bala Mohammed Kauran Bauchi yayi zargin cewa shirin Social Investment kamar yadda gwamnatin tarayya ke aiwatarwa ba komai ba ne illa bututun da wasu yan gata ke amfani da su wajen satar kudi.

Gwamnan ya kuma koka kan rashin wanzuwar shirin zuba jari a jiharsa inda yayi zargin cewa babu wani abu da ya zo jihar da sunan shirin zuba jari ta kowace fuska.

Mohammed ya kuma koka da yadda jihar ta kasa samun maganin da ake bukata wajen rabon tallafin na Covid-19 yana mai cewa har yanzu bai fahimci abin da ke faruwa ba.

Advertisement

Gwamnan ya yi wannan zargin ne a ranar Larabar da ta gabata a wajen kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin gwamnatin jihar a karamar hukumar Dambam da ke jihar.

Senator Mohammed ya bayyana cewa yayin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bullo da shirin da kyakkyawar niyya, wasu masu ruwa da tsaki a harkar aiwatar da shirin suna hana jihar damar cin gajiyar shirin.

Yayin da yake kira ga shugaban kasar da ya kafa wani kwamiti mai karfi don gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin, Bala Mohammed ya yi nuni da cewa irin wadannan shirye-shirye masu karkata akalar jama’a ne da bai kamata a sanya siyasa a ciki ba.

Da yake magana kan shirin karfafa tattalin arzikin jihar, Gwamnan ya bayyana cewa kowace karamar hukuma 20 za ta ci gajiyar kudi Naira miliyan 75 a kokarin samar da ayyukan yi ga jama’a daga tushe.

Shima da yake nasa jawabin, tsohon mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abdul Ahmed Ningi ya ci gaba da cewa yin adalci ga ‘yan kasa zai rage matsalolin tsaro a kasar.

Advertisement