Taskar LabaraiTsaro

Shin Ko Kun San Dr. Gumi Ya Taɓa Share Watanni 6 Tsare A Saudiyya Bisa Zargin Alaƙa Da Ƴan Ta’adda?

2010: Hukumomi a ƙasar Amurka sun gano cewa mutumin nan dan Najeriya mai suna Farouk Abdulmutallab yayi musayar sakonnin email da Sheikh Gumi jim kadan kafin yayi yunkurin taba bama-bamai a wani jirgin Amurka a shekarar 2010, ana gab da jajibirin kirsimeti.

A shekarar 2010 ne gwamnatin Saudiyya ta kama shahararren malamin addinin Islama da ke zaune a garin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, tare da tsare shi sama da watanni 6 bisa zarginsa da alaka da wani dan Najeriya da ke da hannu a harin bam kuma dan ta’adda, Farouk Abdumutallab.

An bayyana cewa an kama Gumi ne a watan Fabrairun 2010 a Makka bisa bukatar gwamnatin Amurka kan musayar sakwannin email da Abdulmutallab.

An kama malamin addinin Musuluncin da a halin yanzu yake fafutukar ganin an yi wa ‘yan bindiga a Najeriya afuwa, bayan da jami’an tsaron Amurka suka yi bincike akan Abdulmutallab.

An kuma gano cewa Abdulmutallab a lokacin yayi magana da Sheikh Gumi jim kadan kafin yayi yunkurin tayar da bam a jirgin sama a ranar 25 ga Disamba, 2009 a Amurka.

An fara kai Gumi Jeddah amma aka mayar da shi Makka aka tsare shi na tsawon watanni 6 kafin gwamnatin Najeriya ta shiga tsakani a sake shi.

Abdulmutallab, mai shekaru 23 a lokacin, bai yi nasara ba lokacin da yayi kokarin tada wani bam da aka saka a cikin gajeren wando sa cikin jirgin Northwest Airlines wanda ya tashi daga Amsterdam dake shirin sauka a Detriot, Michigan dauke da mutane 289.

Na’urar bam din ta gaza tashi, amma Abdulmutallab ya fara ci da wuta da ta bazu zuwa bango da kuma kafet din jirgin.

Fasinjoji hudu ne suka yi gaggawar hana shi tare da taimakawa wajen kashe gobarar, kamar yadda shaidu suka ce, kuma an raka shi zuwa sashen na matakin farko na jirgin tare da mika shi gahukumomin Amurka a lokacin da ya sauka.

Daga baya Abdulmutallab ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a kotun cewa ya tafi kasar Yaman kuma yana da matukar kwarin gwiwa wajen shiga irin wannan makirci na limamin ‘yan gwagwarmayar nan dan asalin kasar Amurka, Anwar al-Awlaki, wanda wani hari da jiragen yakin Amurka suka kashe a kasar Yemen a shekarun baya.

Back to top button