Labarai

Shin Burkina Faso Na Kan Hanyar Wani Sabon Juyin Mulki Ne?

Rikicin baya-bayan nan da aka yi a fadar shugaban kasa, sannan kuma a wurin wani gidan yada labarai da ke Ouagadougou babban birnin kasar, na kara ruruta wutar ra’ayin cewa, Burkina Faso za ta iya komawa wani hali na ayyukan ta’addanci, a daidai lokacin da ake fama da matsalar tsaro a kasar.

Shugaban soji, Captain Ibrahim Traore, – ko “IB” kamar yadda ake kiransa a cikin gida – ya yi alkawarin tabbatar da tsaron kasar da ke fama da rikici a yammacin Afirka, da gudanar da zabe, da kuma gaggauta mika mulkin kasar zuwa dimokuradiyya a lokacin da ya fara kwace mulki a juyin mulki a shekara ta 2022. Juyin mulkin ya biyo bayan mamayar da sojoji suka yi tun farko a makwabciyarta Mali da Guinea.

Sai dai kuma a farkon watan Yuni Traore ya sanar da tsawaita wa’adin mika mulki na tsawon shekaru biyar, saboda ci gaba da samun rashin tsaro a yankunan arewa maso gabashin kasar, inda sojoji ke fafatawa da wasu kungiyoyi biyu masu dauke da makamai da yanzu haka suna rike da kusan rabin kasar Burkina Faso. Abin da yasa wasu suke zargin Traore da yin amfani da kalubalen tsaro wajen kokarin tsawaita wa’adin mulkin shi.

Sai dai abubuwan da suka faru na baya-bayan nan sun sanya ayar tambaya kan ikonsa, da kuma ko me gwamnatin Burkina Faso za ta iya yi domin dakile duk wata barazana ta cikin gida, in ji manazarta.

Me ya faru ranar 11 ga watan Yuni?

A yayin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada da kasar ke yi da kungiyoyin masu dauke da makamai masu alaka da al-Qaeda da ISIL (ISIS), wani manazarci a birnin Ouagadougou wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya fada Al Jazeera cewa mummunan asarar da sojojin Burkina Faso suka yi a watan Yunin 2024 ya kara nuna rashin gamsuwa da sojojin kasar ga gwamnatin Traore.

A ranar 11 ga watan Yuni ne mayakan kungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) suka kaddamar da hare-hare kan dakarun da ke sansanin sojoji a kauyen Mansila da ke kusa da kan iyaka da Nijar a yankin arewa maso gabashin kasar Burkina Faso.

An kashe sojoji da dama kimanin 107 a harin, a cewar bayanan JNIM a wannan makon. Manazarta sun ce yana daya daga cikin koma baya mafi muni, ta fuskar asarar da sojoji suka fuskanta tun bayan barkewar fadan da aka gwabza daga makwabciyar kasar Mali a shekarar 2015.

Advertisement