Taskar LabaraiTsaro

Sheikh Gumi Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Ƴanzu Ƴan Bindiga Ke Kashe Mutane

Yan bindiga na cikin wadanda ke neman ayi musu adalci - Inji Sheikh Gumi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa wani abu ne ya sanya ‘yan bindiga suka fara kashe mutane.

Gumi yace ‘yan fashin sun yi niyyar daukar fansa ne akan kisan ‘yan uwansu da sojoji suka yi ta hanyar kai musu hari ta sama.

Da yake jawabi a wajen wani taron akan koma baya kan harkokin tsaro na bai daya da gidauniyar Global Peace Foundation da Vision Africa suka shirya a Abuja, malamin addinin musuluncin da ke Kaduna yace ‘yan bindigar sun kasance wadanda ke neman adalci.

Ya yi nuni da cewa yana da kyau gwamnatin tarayya ta gana da ‘yan bindiga cikin gaggawa kafin a shawo kan su.

Gumi yace: “Duk mun san cewa ‘yan bindiga ba sa kashe mutane tun farko. Suna sace mutane ne kawai don su sami kuɗi, amma wani abu ya sauya kuma ya mai da su wani dodo na Frankenstein da ke kashe mutane don jin daɗinsa kawai.”

Gumi, wanda ya shahara wajen kare ‘yan bindiga, ya sha alwashin daina ganawa da su.

Malamin addinin Musuluncin ya dauki matakin ne biyo bayan umarnin ‘yan bindiga da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi.

Back to top button