Al'umma

Shari’ar Kisan Hanifa: Kotu tayi fatali da kalaman babban wanda ake zargi Abdulmalik Tanko

Wata babbar kotun jihar Kano karkashin mai shari’a Na’abba Usman, ta yanke hukuncin cewa ‘yan sanda ba su azabtar da wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar, Abdulmalik Tanko ba, a lokacin da yake tsare.

Babban wanda ake zargin a zaman na karshe ta bakin babban Lauyan sa, Usman Labaran, yayi zargin cewa ‘yan sanda sun gana masa azaba a yayin da ake karbar bayanai daga gare shi.

Wannan ya haifar da kira don gwaji-cikin gwaji.

Advertisement

Zaman na ranar Laraba dai shine don tantance ko da gaske ne, ‘yan sanda sun azabtar da wanda ake zargin Abdulmalik Tanko da wanda ake tuhumar sa.

Da yake yanke hukunci kan lamarin, Mai shari’a Usman Na’abba, yace babban wanda ake zargin bai shaida wa kotu na’urar da aka yi amfani da ita wajen azabtar da shi ba.

Yace, shaidun biyu suka gabatar a kan wadanda ake zargin sun fi inganci.

Don haka alkalin kotun ya ce an fitar da bayanan wadanda ake zargin ne bisa radin kansu ba a tursasa su ba.

A cigaba da shari’ar, lauya mai shigar da kara, Musa Lawal ya gabatar da wasu shaidu biyu, wadanda dukkansu ‘yan sanda ne, wadanda suka karanta bayanan da suka zayyana daga wadanda ake zargin a gaban kotu.

Wanda ake kara na biyu, Hashimi, yace bayanin da aka karanta a gaban kotu ba a ciro shi ba.

Lauyan wadanda ake kara Usman Labaran, ya ce za su bude kariyar su, da zarar lauyan da ke kara ya rufe karar nasu.

Ya kuma yi maraba da hukuncin da aka yanke wa wadanda yake karewa.

Lauyan mai shigar da kara, Musa Lawal, yayin da yake nuna jin dadinsa da hukuncin da aka yanke a shari’ar da ake yi a shari’ar, ya ce sun gabatar da shaidu kusan bakwai, kuma suna fatan rufe karar a zaman na gaba.

Mai shari’a Usman Na’abba ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga Maris 2022.

Advertisement