Taskar Labarai

Bala Lau, Yayi Kira Ga Jami’an Tsaro Da Su Hana Kiristoci Kona Masallatai Da Dukiyoyin Musulmi

Shugaban kungiyar wa’azin musulunci ta IZALA Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga jami’an tsaro, musamman hukumar ‘yan sanda, da suyi gaggawar hana kiristoci kona masallatai da dukiyoyin su a garin Billiri dake jihar Gombe.

Shehin Malamin yace,abun takaici ne kwarai, akan batun nada sabon sarki wanda ba’a kai ga sanarwan ba, amma haka al’ummar kiristoci na Garin Billiri suka fito sukayi ta kona masallatai da dukiyoyin al’umnar musulmi ba gaira babu dalili.

Sheikh Bala Lau yace idan an bibiyi tarihin sarautar billiri, musulmi sukayi shekaru dari da uku suna mulki a kasar billiri ba tare da zaluntar kiristoci ba, sai a shekarar 2001 a mulkin marigayi Habu Hashidu bayan mutuwar sarki musulmi aka nada sarki kirista, kuma haka musulmai suka hakura ba tare da tayar da hankalin kiristoci ba. Sai yanzu da ake hasashen musulmi ne zai zama sabon Sarki, kafin sanarwa suka farwa musulmai sukayi ta kone kone, menene hadin musulmai da batun sanar da sarauta tunda aikin gwamnati ne? Menene yasa tun laraba kiristoci Suke barazanar farwa musulmai amma jami’an tsaro basu dauki mataki ba sai da aka farwa musulmai aka kona masallatai da dukiyoyin Su? Menene yasa ake farfasa masallacin kofar sarki a gaban jami’an tsaro amma basu hana ba?

Sheikh Bala Lau yayi kira ga gwamnatin jihar Gombe da ta kara kokari akan wanda takeyi, kuma kada ta janye akan niyyarta na zaban Sarkin da ya dace, tunda majalisar zaban sabon Sarkin Billiri sun zabi mutum uku, sannan kamar yadda doka ta tsara, sun baiwa gwamnan jihar Gombe, shi kuma doka ta bashi damar ya zabi wanda yake so daga cikin ukun, bai kamata hakan ya zama fitina ba, indai ba shiryeyyen lamari ne tada fitinar ba.

wanda mahaifinsa musulmi shine ya rasu, sannan aka baiwa Sarki kirista a shekarar 2001, shima kiristan ya mutu, yanzu kuma ake Ikikarin zabar musulmi a matsayin sabon sarki, amma shine kiristoci suke ta wannan da’addanci tunda Musulmi ne.

A karshe Shehin Malamin ya yabawa gwamnan jihar Gombe a maganar da yayi a yammacin asabar dinnan a kafafen yada labaru, inda yace zai kamo masu hannu a cikin wannan rigimar kuma za’a hukunta su matukar an same su da laifi, sannan ya kara tabbatar da cewa shi doka ta baiwa dama ya zabi sabon sarki, kuma ba gudu babu ja da baya zai zabi wanda ya dace.

Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau
Shugaban JIBWIS ta Naijeriya.
media@jibwisnigeria.org
08-Rajab-1442
20-February-2021.

JIBWIS NIGERIA.

Daga Ibrahim Baba Suleiman.

Back to top button