Al'umma

Sauyin yanayi na tilastawa ƴan mata a ƙasar Zimbabwe shiga harkar karuwanci

Galibin yankunan kasar Zimbabwe na fama da matsalar sauyin yanayi tare da zafafar yanayi

Nkuruma, mai shekaru 16, yana duban sararin samaniya cikin nutsuwa yayin da rana ta fadi, yana shirin yin aiki yayin da dare ya fara.

Nkuruma, wadda muka canza sunan ta domin kariya, na cikin daruruwan yan mata daga yankunan karkarar Zimbabwe da suka shiga harkar karuwanci a shekarun baya-bayan nan a cikin birane.

Muna jira har sai magariba tayi mu fara aiki. Galibi abokan cinikin mu waɗanda muke karewa ne saboda ba sa son a gan su kamar yadda mutum yayi aure wasu kuma mutane ne masu daraja a cikin al’umma. In ba haka ba, muna buɗewa na sa’o’i 24,” in ji Nkuruma.

Advertisement

Jim kadan bayan rasuwar iyayenta, ta daina karatu saboda kakarta ta kasa biyan kudin. Bayan shafe shekaru ana fama da fari da rashin amfanin gona, Nkuruma ta kasa ganin makoma a karkara, lamarin da ya sa tana da shekaru 14 ta koma babban birnin Harare domin neman ingantacciyar rayuwa.

“Na zo nan a matsayin mai kula da jarirai. Na yi wata shida ina aikin kuyanga, amma ba ta samun riba. Lokacin da cutar ta COVID-19 ta fara, ta yi muni saboda matar da nake yi wa aiki ta rage mini karancin albashi. Don haka na bar aikin,” in ji ta.

Nkuruma ba ta so komawa gida ta koma Epworth, mai tazarar kilomita 12 daga Harare babban birnin kasar, inda bayan ta hadu da kawayen ta aka soma yin lalata da ita.

Garin yayi kaurin suna wajen tashe-tashen hankula, karuwanci, da muggan kwayoyi tare da yawan jama’a da ke cigaba da karuwa tare da ƙaura zuwa birane.

Nkuruma da sauran yan mata matasa sun taru a wani wuri da aka fi sani da “booster”, inda wata doguwar hasumiya ta sadarwa ta harba zuwa sama. A cikin rana, wurin yayi tsit, da mutane kaɗan. Amma da zarar dare yayi, to, kudan zuma ne na ayyuka yayin da karuwai ke neman abokan ciniki.

Catherine Masunda, wacce ta kafa kungiyar Youth 2 Youth, wata kungiya mai zaman kanta a birnin Harare, ta ce yayin da kididdigar yawan yan matan da ke karuwanci ke da wuya a iya kididdige su, lamarin yana da matukar damuwa.

Advertisement