Al'umma

Saurayi Ya Mayar Wa Gwamnatin Kano Albashin Mahaifin Shi Marigayi

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa wani Yusuf Sulaiman Sumaila, bisa mayar da albashin da ya karba ta asusun mahaifinsa da ya rasu zuwa asusun gwamnati.

Sumaila ta samu yabo ne a cikin wata sanarwa da Abdullahi Ibrahim, mai magana da yawun gwamnan kan kafafen yada labarai na zamani, ya fitar ta shafin sa na X.

Mahaifin Sumaila ya rasu a watan Oktoban 2022 amma gwamnatin jihar ta ci gaba da biyansa albashi har zuwa watan Agustan 2023.

Sai dai bayan lura da halin da ake ciki Sumaila ya mayarwa gwamnatin jihar albashin domin sanar da ita cewa mahaifinsa ya rasu shekara daya da ta wuce ya kuma mayarwa gwamnati da kudaden da suka kai N328,115.75.

“Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ci gaba da biyan albashin mahaifinsa da ya rasu a cikin asusunsa bayan rasuwarsa a watan Oktoban 2022 har zuwa watan Agustan 2023, inda ya nemi a dakatar da biyan albashin,” in ji Yusuf.

“Don gamsuwa da gwamnan, Yusuf ya kuma bukaci a mayar wa gwamnati kudaden da suka kai 328,115.75, wanda gwamnan da kan sa ya gayyace shi ofishin sa don yi masa godiya.”

Kakakin ya ce gwamnan ya yabawa Yusuf bisa wannan gagarumin karimcin da ya nuna, inda ya bukaci sauran matasa da su yi koyi da shi, su kuma kiyaye kimar gaskiya.