Labarai

Sanusi Lamido Yayi Watsi Da Umarnin Kotu, Ya Naɗa Rawanin Sarauta

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya hau kujerar fada, yana karbar gaisuwar sarauta.

Wannan lamari dai ya zo ne duk da cewa hukumar tsaro ta hadin gwiwa a jihar Kano ta bayyana cewa suna bin umarnin kotu da ya hana a dawo da sarkin.

Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda ya fito daga cikin fadar sarki zuwa waje, inda a al’adance sarakuna ke karbar al’amuransu tare da gudanar da zaman majalisar, daruruwan magoya bayansa ne suka taya shi murna yayin da ya hau doki.

Tun da farko mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya shaida wa manema labarai cewa “babu wanda zai iya sauya matsayin su kan maido da Muhammadu Sanusi II saboda sun yi shi bisa ka’ida.”

Ya ce, “Abin da ake kira umarnin kotu na hana su mayar da Sanusi ba a hukumance aka mika musu ba, kuma kamar yadda a lokacin da suka yi aikin dawo da shi, sai bayan sa’o’in aiki ne, wanda hakan ya nuna cewa duk wani abu da ya fito daga kotu a kan haka. tuni ya makara.”