Taskar Labarai

Sanusi Lamido Ya Yabawa Ganduje Akan Hana Sheikh Kabara Yin Wa’azi A Kano

Tsohon sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi II wanda gwamnatin Jahar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sauke a watan maris din shekarar 2020, ya jin-jinawa Ganduje bisa dakatar Shehin Malamin Darikar nan Sheikh Nasiru Kabara daga yin wa’azi a Kano, saboda ana zargin sa da yin hudubobi domin masu tada tarzona da kuma suka sabawa addinin musulunci.

Sanusi Lamido yayi wannan jin-jinawar ne a lokacin da yake jawabi a wata muhadara (Lecture) da ya gabatar a babbar jami’ar London (Oxford).

Matakin da gwamnatin Kano ta dauka na hana malamin nan wanda ake cece-kuce akan sa yin wa’azi mataki wanda za’a yabawa gwamnati. Mutane Kano mutane ne masu kokarin bin tafarkin sunna, kana an san su da bin tafarkin da Shehu Usmanu Bin Fodio ya tafi akai.” Inji Sanusi.

Haka zalika Shehu Bin Fodio mutam ne wanda yake bin sunnar Manzon Allah (Sallahu Alaihi Wasallam) sau sa kafa, don haka mutanen kano ba zasu lamunci wani mutum ya kawo wasu kirkire ba (Bid’a a cikin addinin musulunci ba.”

Daga karshe Sanusi yayi kiran da a yabawa wannan kokari na gwamnatin Ganduje.

Back to top button