Taskar Labarai

Sama Da Shaguna Dubu 9,500 Suka Gone A Babbar Kasuwar Sakkwato – Tambuwal

Gwamnatin Jahar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal a yau Litinin, ya bayyanawa kwamitin da Shugaban kasa Muhammadu ya wakilta domin ja-jantawa mutanen da bala’in gobara a babbar kasuwa ya aukawa a satin da ya gabata cewa akalla sama shaguna 9,500 iftila’in gobarar ya shafa a kasuwar wadda ke da kimanin shaguna 16, 000.

Kwamitin ja-jantawa daga gwamnatin tarayya wanda ya samu shugabancin babban shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa, furofeso Abdullahi Gambari, ya shaidawa gwamnatin sakwwato karkashin jagorancin Tambuwal cewa Buhari yayi alkawarin taimakawa gwamnatin jaha domin sake gina babbar kasuwar.

Tambuwal yayi fadi kimanin adadin shagunan da suka kone ne wadanda yace sun kai adadin 60% cikin 100% na kasuwar, baya ga asarar dukiyoyi na miliyoyin naira da akayi duk a satin da ya gabata, yayin godiya ga shugaban kasa kan tunawa da mutanen sakkwato a cikin irin wannan lokaci na jimami.

Idan muka kasafta 60% daga cikin kashi 100% na kasuwa mai adadin shaguna 16,000, zamu samu cewa kashi 60% yana a madadin shaguna 9,600.

Advertisement