Sallar Nafila Lokacin Da Liman Ya Hau Mimbarin Juma’a
1 – Idan mutum ya shiga masallaci ranar Jumu’ah liman yana akan mimbari, zai yi sallah raka’a biyu, amma ya gajarta tsayin. (Bukhari da Muslim).
2 – Idan mutum ya tarar da ana kiran sallah kafin a fara huduba, zai yi sallah lokacin da ake kiran sallar ba zai jira sai an gama kiran sallah ba, saboda sauraron huduba wajibi ne, amma sauraron mai kiran sallah Sunna ne. (Ibn Uthaimeen)
3 – Idan mutum bai samu shiga masallaci ba ya tsaya a harabar masallaci, ba zai yi sallah ba lokacin da liman ke huduba, saboda sallar ta Tahiyyatul masjid ce, bata wajaba sai ga wanda ya shiga masallaci.
4 – Mutane da yawa sukan yi kuskure sai su zata akwai wasu raka’ah biyu da ake yi kafin jumu’a, sai kaga mutum yazo yana wajen masallaci ya kabbarta sallah alhali liman yana huduba. Wannan kuskure ne, matsayin sa kamar wanda ya tashi a cikin masallaci ya kabbarta sallah alhalin liman yana huduba.
5 – Duk wanda ya shiga masallaci wajibi ne (a kan zance mafi inganci) yayi sallah raka’ah biyu kafin ya zauna. Wannan hukuncin da ranar jumu’ah da Assabar da sau ran ranaku duka daya ne. Dalili akan hakan shine, cewar da Manzon Allah S.A.W. yayi: Idan dayan ku ya shiga masallaci kada ya zauna sai yayi sallah raka’a biyu. (Bukhari da Muslim)
Ya kamata a yi fadakarwa ga mutane akan wannan hukuncin, saboda da yawa akan saɓa.
Tare Da: Sheikh Jabir Sani Maihula