Taskar Labarai

Sakkwato: Gwamnatin Tambuwal Ta Soke Wasu Kwangiloli Da Aliyu Wamakko Ya Bayar A Lokacin Yana Gwamna

Gwamnatin jahar sakkwato karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal ta soke wasu kwangiloli da gwamnatin ta shude a lokacin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko yana gwamna saboda rashin aiwatar da kwangilolin kamar yadda aka rubuta a takardun kwangilolin.

Kwangilolin da aka soken sun hada da kwangilar gina babbar asibiti a karamar hukumar Wammako, da Sanata Wamakko ya bayar a shekarar 2013.

Jawabin soke kwangilolin ya biyo bayan kammala mitin na zababbu da ake yi a duk karshen kwana bakwai wanda Tambuwal ke jagoranta.

Har wa yau a wurin mitin din an amince da fitar da kudi har naira biliyan hudu (N4,000,000,000) domin gina wuraren ayyukan lafiya da tare da na harkar ilimi guda daya, sannan kuma aka soke wasu jerin kwangiloli guda huda wadanda aka yi ko -in-kula da su.

Advertisement