Wasanni

Sadio Mane Ya Bayyana Wanda Ya Gaya Masa Ya Koma Al-Nassr

Sadio Mane ya bayyana wanda ya ba shi shawarar ya zama dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya.

Sadio Mane ya kammala barin Bayern Munich zuwa kungiyar Al Nassr ta Saudi Pro League, inda a yanzu yake karbar fam 650,000 a mako.

Mane ya sanya hannu kan kwantiragi har zuwa 2027 wanda ke nufin zai samu kusan fam miliyan 136 gaba daya idan ya ga yarjejeniyar.

Dan wasan mai shekaru 31 ya koma Bayern ne a bazarar da ta wuce kan yarjejeniyar shekara uku da Liverpool.

Sai dai ya rasa gurbinsa a kungiyar sakamakon wani lamari da ya faru inda ya buga wa abokin wasansa Leroy Sane naushi bayan rashin nasara a hannun Manchester City a gasar cin kofin zakarun Turai a watan Afrilu.

An cire Mane daga cikin ‘yan wasan da kuma ci tararsa yayin da Bayern ta lashe kofin Bundesliga karo na 11 a jere. Dan wasan ya ci kwallaye 12 a wasanni 38 da ya buga.

An danganta dan wasan mai shekaru 31 da kungiyoyin Turai da dama, ciki har da Chelsea, wadanda aka ce suna sa ido a kansa a watan Afrilu.

Sai dai duk da haka, Mane ya zabi kulla yarjejeniya da Al-Nassr, saboda bukatar mahaifiyarsa a matsayin dalilin yanke shawarar shiga tawagar kasar Saudiyya.

“Iyalina sun karfafa ni in zo Saudiyya, musamman da yake kasar Musulmi ce,” in ji Mane (ta hanyar EuroFoot). “Mahaifiyata ta yi farin ciki sosai kuma ta dage cewa na zabi Al-Nassr.”

Free Bonus

X