Lafiya

Sabuwar dokar Uganda zata sanya tara ga waɗanda suka ƙi karɓar rigakafin COVID-19

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda

Gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni na sake duba wata doka don sanya tara da kuma dauri a kan mutanen da suka ki allurar COVID-19.

Uganda na shirin sanya tara akan mutanen da suka ki yarda a yi musu allurar rigakafin cutar ta COVID-19 kuma wadanda suka kasa biya za’a iya tura su gidan yari a karkashin wani gyara na dokar kiwon lafiyar jama’a da ake nazari a yanzu a majalisar dokokin kasar.

Ministar lafiya Jane Ruth Aceng ta fadawa yan majalisar a ranar Litinin cewa gyaran yana da mahimmanci don soke abubuwan da aka daina amfani da su, da sake duba tarar laifukan da aka aikata da kuma kare yan kasa.

Advertisement

“Kudirin yana da wani sashe kan alluran rigakafi da rigakafi a matsayin matakin kiwon lafiyar jama’a don kare masu rauni,” in ji ta. “Lokacin da muka gabatar da sabbin alluran rigakafi, muna buƙatar samun tarin mutane don haka mu samar da rigakafi mai yawa. Yana da mahimmanci cewa duk wanda ya kamata a yi wa allurar, an yi masa allurar.”

Advertisement