Siyasa

Sabon rikici ya barke a APC, yayin da gwamnan Niger ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar

Rikicin shugabancin da ya kunno kai a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na makwanni yanzu ya dauki wani salo daban a ranar Litinin a Abuja lokacin da Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Bello, ya iso sakatariyar jam’iyyar ta kasa domin ya zama Shugaban Kwamitin Tsare-tsare na Riko/Babban Taro.

Bello, wanda ya isa wurin a cikin tsauraran matakan tsaro da ya kunshi jami’an tsaro kusan 70 da motocin sintiri da basu gaza 15 ba, wadanda suka tare hanyoyin shiga harabar, yace ya samu albarkar shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya).

A cewar shi, zai yi aiki ne a matsayin shugaban CECPC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a halin yanzu yana kasar Dubai bisa dalilan lafiya.

Advertisement

Bello ya bayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da yayi da mambobin CECPC da shugabannin jihohin da ya jagoran ta.

Da aka tambaye shi da ya bayyana sabon matsayin shi a kwamitin, Bello yace “Mukaddashin shugaban na dade ina aiki tun da shugaban yayi tafiya.”

Akan rahotannin korar Mai Mala Buni a matsayin shugaban jam’iyyar, ya amsa da cewa, “Babu wani sharhi.”

Da yake bayyana makasudin ziyarar shi a sakatariyar ta kasa, mukaddashin shugaban yace “Shugabannin jihohin sun yi rantsuwar kama aiki a yau, kuma mun tattauna cigaban da aka samu a taron da kuma abin da ya kamata a yi a gaba domin mu cimma ranar 26 ga Maris, 2022 don Convention na ƙasa.”

A matsayins shi na shugaban riko, Bello ya kuma samu rahoton kwamitin shiyya na jam’iyyar gabanin babban taron kasa na ranar 26 ga Maris.

A baya mun rahoto cewa an kafa kwamitin shiyya a ranar Talatar da ta gabata tare da gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a matsayin shugaba.

A cewar jam’iyyar APC, an kaddamar da kwamitin ne domin tabbatar da tsarin rabon mukaman shugabanci na gaskiya da adalci a dukkanin shiyyoyin siyasar kasar nan.

Advertisement