Siyasa

Sabon mataimakin gwamnan Zamfara Nasiha yayi murabus daga majalisar dattawa

Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya, Muhammad Nasiha, yayi murabus daga mukamin shi na sanata a majalisar dattawa a hukumance.

Advertisement

Hakan ya biyo bayan nadin da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara yayi mai a matsayin mataimakin shi.

Nasiha ya maye gurbin Mahadi Ali, wanda majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige a makon jiya.

Advertisement

Da yake karanta wasikar da aka aikawa majalisar dattawa a zauren majalisar, shugaban majalisar, Sanata Ahmed Lawan, ya sanar da murabus din Nasiha ga majalisar.

Advertisement