Tsaro

Rwanda za ta sake bude kan iyaka da Uganda yayin da alakar su ta yi tsami

Shugaban kasar Rwandan

Rwandan – A ranar Litinin ne kasar Rwanda za ta sake bude wata mashigar kan iyaka da Uganda da aka rufe kusan shekaru uku da suka gabata, duk da cewa ana takun saka tsakanin kasashen tsakiyar Afirka da ke makwabtaka da juna, sakamakon zargin leken asiri da goyon bayan yan adawa.

Advertisement

Rwanda ta sha zargin Uganda da goyon bayan kungiyoyin ‘yan tawaye da ke shirin hambarar da gwamnati a Kigali yayin da Kampala ta zargi Rwanda da gudanar da ayyukan leken asiri ba bisa ka’ida ba a Uganda.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafin Twitter a ranar Juma’a, ma’aikatar harkokin wajen Rwanda ta ce kasar za ta sake bude kan iyakarta a ranar 31 ga watan Janairu.

Advertisement

“Rwanda ta lura da cewa akwai wani tsari na warware batutuwan da Rwanda ta gabatar, da kuma alkawurran da gwamnatin Uganda ta dauka na magance sauran matsalolin,” in ji sanarwar.

Ƙoƙari daban-daban, gami da  ƙoƙarin sasanci   Angola, don maido da alakar da aka saba yi da buɗe kan iyaka bai yi nasara ba.

Rufe kan iyaka a watan Maris na 2019 ya kawo cikas ga alakar kasuwanci a yankin.

Advertisement