Ronaldo Ya Samu Kyakkyawar Tarba A Iran

Dubban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Iran ne suka yi wa Cristiano Ronaldo tarba mai ban mamaki a ranar Litinin a yayin da tawagarsa ta Saudiyya ta isa Tehran a wasan farko na gida da waje tun bayan da kasashen biyu suka dawo da huldar jakadanci.
Magoya bayansa sun yi ta rera taken dan wasan na Portugal wanda ya taba zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya sau biyar a lokacin da ya isa tare da takwarorinsa na Al Nassr don karawa da kulob din Persepolis na Iran a gasar cin kofin nahiyar Asiya ranar Talata.
Wasan zai kasance na farko tun bayan da Tehran da Riyadh suka cimma yarjejeniya tsakanin China da aka sanar a watan Maris.
Kungiyoyi daga kasashen biyu sun buga wasanni ne kawai ba tare da tsangwama ba tun shekarar 2016 lokacin da Saudiyya mai rinjayen Sunni da Iran mai rinjayen Shi’a suka yanke alaka.
A birnin Tehran, murna ta cika yayin da magoya bayanta ke dakon kallon Ronaldo a lokacin da yake barin filin jirgin saman Imam Khumaini na Iran.
Dubban magoya bayansa ne suka yi dafifi a kan tituna yayin da Ronaldo da tawagarsa suka isa wani otel da ke birnin Tehran a cikin wata motar safa.
Wasu kuma suna rera taken “Ronaldo, Ronaldo!” har ma ya mamaye harabar otal din.
Fatocin Ronaldo sun taso a manyan titunan babban birnin kasar Iran dauke da “Maraba”, da aka rubuta da Larabci, da Ingilishi da kuma Farisa.
Navid Borhanifar, mai shekaru 28, mai son Ronaldo ya ce “Ina tsammanin zai zama wasa mai kyau kuma zai yi farin ciki sosai.”
“Yana da ban sha’awa sosai a gare ni.”
Abin bakin ciki ga magoya bayansa, ba za a bari kowa ya halarci wasan da za a yi a katafaren filin wasa na Azadi, wanda zai dauki nauyin mutane 90,000.
Hukumar Kwallon Kafa ta Asiya ta yanke hukuncin cewa a buga wasan a bayan fage a matsayin ladabtar da wata takaddama ta 2021 da Persepolis ta buga a yanar gizo kafin wasan da wata tawagar Indiya.