Siyasa

Rikici ya ɓarke a sansanin Osinbajo kan batun tarihin rashin lafiyar Buhari

Takaddama ta biyo bayan wata sanarwa da wani Olugbenga Olaoye, wanda shi ne mai hada kan ‘Osinbajo Think Tank’ da ya fitar da ke magana kan tarihin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanarwar ta janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.

Kalaman na Olaoye sun jawo fushin wasu magoya bayan Osinbajo.

Amma mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, ya bukaci jama’a da su yi watsi da kalaman kungiyar ‘Osinbajo Think Tank’.

Olugbenga Olaoye, wanda shi ne mai shirya kungiyar “Osinbajo Think Tank”, yayi wata hira ta gidan talabijin na Arise TV inda ya bayyana lafiyar Buhari a matsayin daya daga cikin dalilan da suka sa za’a zaɓi Osinbajo a matsayin shugaban kasa a 2023.

“Dukkan mu mun san abin da ya faru da shugaban kasa Muhammadu Buhari a farkon gwamnatin shi,” in ji Olaoye.

“Ya shafe tsawon lokaci baya Najeriya saboda rashin lafiyar shi.”

Yace hakan ya bada damar “wasu mutane” su kwace harkokin kasar daga hannun shugaban kasa.

Sai dai Akande yace Olaoye da kungiyar shi ba su wakiltar mataimakin shugaban kasar wanda a ranar Litinin din da ta gabata ya bayyana bukatar shi ta ya gaji Buhari a ofis.

“Hakika wannan mai magana baya wakiltar VP ko ofishin shi,” in ji Akande.

“Ra’ayin shi wannan gaba daya ne.” Laolu ya wallafa a Twitter.

Ban ma san da akwai wata kungiyar”Osinbajo Tink Tank” ba, in ji Akande.

Back to top button