Kasuwanci

Rikici Na Ƙoƙarin Ɓarkewa Tsakanin Bauchi Da Gombe Akan Sabuwar Rijiyar Mai

Da alama dai ana ta samun rikici kan mallakar rijiyar mai ta Kolmani yayin da Jihohin Bauchi da Gombe suka fara yin ikirarin mallakar rijiyar mai ɗin, kamar yadda jaridar Vanguard News ta habarto.

Jami’ai da mazauna jihohin biyu sun kuma zargi juna da yunkurin daidaita wurin da aka ce yana dauke da gangunan danyen mai biliyan daya da iskar gas mai cubic biliyan 500.

Wannan cigaban na zuwa ne bayan makonni biyu da shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya kaddamar da aikin hako mai a rijiyar mai ta Kolmani da kamfanin mai na Nigeria National Petroleum Corporation Limited da abokan huldar sa suka gudanar.

Advertisement

Kolmani a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na da man fetur na kasuwanci mai lamba 809 da kuma 810, inda ya yanke a yankin Kolmani Daya, Biyu, Uku, Hudu da Biyar.

Advertisement